‘Yan Sanda Sun Cafke Wanda ake Zargi da Kashe Mawakin Gargajiya

Written by

in

‘Yan sanda a ƙaramar hukumar Tafawa Balewa ta jihar Bauchi sun kama wani mutum da ake zargi da hannu a kisan fitaccen mawaki, John Zuya Zuya, wanda ya shahara a tsakanin al’ummar Sayawa.

Rahotanni sun bayyana cewa marigayin ya rasu ne bayan dawowarsa daga Lagos, inda ya gudanar da wani gagarumin bikin nishadi tare da masoyansa.

Ana zargin wani abokinsa mai suna Emmanuel Wakili da kisan, bisa rahotannin da ke cewa an samu sabani tsakaninsu saboda kishi.

Hukumar ‘yan sanda ta tabbatar da cewa bincike na ci gaba domin gano cikakken abin da ya faru.

Comments

13 responses to “‘Yan Sanda Sun Cafke Wanda ake Zargi da Kashe Mawakin Gargajiya”

Leave a Reply