Blog

  • ‘Yan Sanda Sun Cafke Wanda ake Zargi da Kashe Mawakin Gargajiya

    ‘Yan sanda a ƙaramar hukumar Tafawa Balewa ta jihar Bauchi sun kama wani mutum da ake zargi da hannu a kisan fitaccen mawaki, John Zuya Zuya, wanda ya shahara a tsakanin al’ummar Sayawa.

    Rahotanni sun bayyana cewa marigayin ya rasu ne bayan dawowarsa daga Lagos, inda ya gudanar da wani gagarumin bikin nishadi tare da masoyansa.

    Ana zargin wani abokinsa mai suna Emmanuel Wakili da kisan, bisa rahotannin da ke cewa an samu sabani tsakaninsu saboda kishi.

    Hukumar ‘yan sanda ta tabbatar da cewa bincike na ci gaba domin gano cikakken abin da ya faru.

  • Kotu Ta Sanya Ranar 30 ga Oktoba Don Gurfanar da Mutum 5 da Ake Zargi da Cin Mutuncin Sanata Shehu Buba a Intanet

    Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta sanya ranar 30 ga Oktoba, 2025 domin gurfanar da wasu mutane biyar da ake zargi da aikata laifin cin mutuncin Sanata Shehu Buba Umar ta kafafen sada zumunta. Sanatan shi ne shugaban Kwamitin Majalisar Dattawa kan Tsaro da Leken Asiri.

    An shirya gurfanar da su a gaban Mai Shari’a Rita Ofili-Ajumogobia a ranar Talata, inda ake sa ran za su bayar da amsar tuhume-tuhumen da ake musu. Sai dai, rashin halartar alkalin ya sa aka dage shari’ar zuwa ranar 30 ga Oktoba.

    Lauyan gwamnati, Anthony Egwu, da lauyoyin wadanda ake tuhuma — Hamza Dantani da Affis Matanmi, sun halarci zaman kotun.

    Sunayen wadanda ake tuhuma sun hada da:

    1. Ahmed Abdulrahman (41 shekara)
    2. Daure David (35 shekara)
    3. Ishaq Muhammad (25 shekara)
    4. Abdulrashid Musa (30 shekara)
    5. Nasir Abubakar (21 shekara)

    An gurfanar da su ne bisa tuhume-tuhume 11, da Ofishin Sufeto Janar na ‘Yan Sanda (IGP) ya shigar da kara mai lamba FHC/ABJ/CR/526/2025, wadda aka rubuta ranar 3 ga Oktoba kuma aka karɓa ranar 6 ga Oktoba, 2025.

    Tuhume-tuhumen sun shafi laifin cin mutunci ta kafar intanet (cyberstalking) da kuma zamba ta yanar gizo (advance fee fraud) bisa dokar Cybercrime Act 2015 (da aka gyara a 2024).

    A cewar tuhumar farko, ana zargin su da yin yarjejeniya don aikata laifi na cin mutuncin Sanata Shehu Buba Umar ta hanyar intanet, wanda ya sabawa Sashe na 27(1)(b) kuma ake hukunta shi a ƙarƙashin Sashe na 21(1)(b) na dokar.

    A cikin wani tuhunci na daban, ana zargin Ahmed Abdulrahman da yada wani bidiyo a TikTok da YouTube ta asusun “Kibanna Channel” inda ya zargi Sanatan da cewa “mai tallafa wa ‘yan ta’adda ne,” tare da yin kira da a bincike shi. Ana zargin ya san wannan zance ba gaskiya ba ne, amma ya aikata hakan don tayar da hankalin jama’a, sabanin Sashe na 24(1)(5) na dokar Cybercrime Act.

    Haka kuma, Abdulrashid Musa da Nasir Abubakar, wadanda ake tuhuma na 4 da 5, sun nemi afuwa a bidiyo daban-daban da suka fitar bayan sun yarda da laifin cin mutuncin Sanatan Bauchi ta Kudu a kafafen sada zumunta.

    Rahotanni sun nuna cewa hukumomi sun kammala bincike, kuma ana sa ran shari’ar za ta fara ne da karɓar amsar tuhume-tuhume daga wadanda ake zargi a ranar da kotu ta tsara — 30 ga Oktoba, 2025.

  • Elder Karofi ya caccaki Sanata Shehu Buba kan kama matasa

    Wani jigo a cikin matasan jihar Bauchi, Elder Karofi, ya yi kakkausar suka ga Sanata Shehu Buba bisa zargin yin amfani da mukaminsa wajen kama matasa a fadin jihar.

    A cikin wani faifan bidiyo da ya wallafa a safiyar yau, Elder Karofi ya zargi sanatan da amfani da karfin iko wajen tsoratar da matasa maimakon yin aiki tare da su don ci gaban siyasa da dimokuraɗiyya.

    Ya ce siyasa rigar ’yanci ce wacce ta baiwa kowa damar bayyana ra’ayinsa, ba doka ta kama ko tsoratar da mutane ba.

    “Shehu Buba, me kake nema da matasan Bauchi? Kullum sai ka kama wannan ko wancan – wannan abin naka ya yi yawa. Kai ba kai kaɗai ba ne, siyasa ba mallakar mutum ɗaya ba ce. Idan bada ka iya jure adawa ba, ka hakura da siyasa gaba ɗaya,” in ji Elder Karofi a cikin bidiyon.

    Elder Karofi ya kara da cewa matasan Bauchi ba sa tsoron kowa, kuma za su ci gaba da fadin ra’ayinsu da kalubalantar duk wani dan siyasa da ke kokarin tauye hakkokinsu, har ma da Sanata Shehu Buba.

    Ya kuma yi gargadi ga sanatan da ya daina tsoratar da matasa, yana mai cewa:

    “Muna maka gargadi, ka daina tsoratar da matasan Bauchi. Ka bar su su taka rawarsu cikin ’yanci da dimokuraɗiyya.”

  • Tsohon Shugaban Ƙungiyar Daliban ATBU Ya Soki Yunkurin Cire Kalmar “Technology” Daga Sunan Jami’ar

    Tsohon Shugaban Ƙungiyar Daliban Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa (ATBU) Bauchi, Muhammad Aliyu wanda aka fi sani da Songuy, ya bayyana rashin amincewarsa da kudirin da ake yi na mayar da jami’ar daga ta kimiyya da fasaha zuwa jami’a ta gama-gari.

    Songuy ya bayyana wannan yunkuri a matsayin “mataki na komawa baya,” yana mai cewa duniya tana ci gaba cikin sauri ne saboda ci gaban fasaha da kere-kere.

    Ya ce ko da yake a Najeriya ana ganin jami’o’in gama-gari suna taimakawa wajen samar da ma’aikata da inganta tattalin arziki, amma gaskiyar magana ita ce fasaha ce ginshiƙin ci gaban duniya.

    “A yau, duniya tana cigaba ne saboda fasaha. Amma a Najeriya, ana yawan jaddada cewar jami’o’in gama-gari ne ke samar da ma’aikata da bunƙasa tattalin arziki. Amma gaskiya ita ce, fasaha ta fi wadannan abubuwa nesa. Kada mu rikita ci gaba da koma baya,” in ji shi.

    Muhammad Aliyu ya shugabanci Ƙungiyar Daliban Jami’ar ATBU a shekarar karatu ta 2010/2011.

  • Gwamna Bala Mohammed ya amince da dokokin kafa Masarautar Zaar da sabbin masarautu 13 a Bauchi

     

    Gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed, ya rattaba hannu kan wasu muhimman dokoki guda huɗu da nufin ƙarfafa tsarin mulki, inganta masarautu, da tabbatar da walwalar ma’aikata a fadin jihar.

    Daya daga cikin dokokin da aka amince da su ita ce soke dokar kafa Masarautar Sayawa da maye gurbinta da Masarautar Zaar, wacce za ta kasance da hedikwata a kauyen Mhrim Namchi da ke cikin ƙaramar hukumar Tafawa Balewa — domin amsa tsohon buƙatar al’ummar yankin.

    Haka kuma, Gwamna Bala ya sanya hannu kan Dokar Kafa da Dage Sarautu, wacce ta ba da dama ga ƙirƙirar sabbin masarautu guda 13 tare da fiye da dagatai 100 a fadin Jihar Bauchi.

    Bugu da ƙari, ya amince da Dokar Asusun Fansho ta Ƙananan Hukumomi, inda ya sha alwashin biyan basussukan fansho da kudaden giratuti da ake bin tsoffin ma’aikatan ƙananan hukumomi.

    Sannan kuma, Gwamnan ya sanya hannu kan Dokar Ƙarin Kasafin Kuɗi ta Shekarar 2025, domin tallafawa aiwatar da muhimman ayyuka da shirye-shiryen ci gaba da gwamnatin sa ke aiwatarwa.

    Yayin rattaba hannu a gidan gwamnati da ke Bauchi, Gwamna Bala Mohammed ya gargadi jama’a da su guji siyasantar da sabbin dokokin, tare da umartar hukumomin tsaro da su tabbatar da bin doka da oda wajen aiwatar da su.

    A nasa jawabin, Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Bauchi, Rt. Hon. Abubakar Y. Sulaiman, ya yabawa Gwamnan bisa yadda yake amsa buƙatun al’ummomi daban-daban a jihar. Ya kuma bayyana cewa yawan jama’ar da suka halarci zaman sauraron ra’ayoyin jama’a a kan dokokin ya nuna irin kishin al’umma wajen ganin gwamnati ta isa ga ƙananan yankuna.

  • Majalisar Dattawa ta amince da karatu na biyu kan cire “Technology”daga sunan ATBU Bauchi

    Majalisar Dattawa ta amince da karatu na biyu na kudirin da ke neman sauya sunan Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa, Bauchi (ATBU), ta hanyar cire kalmar “Technology” daga cikinsa. Wannan mataki na nufin mayar da jami’ar ta zama jami’a ta gama-gari (conventional university) wacce za ta iya koyar da fannoni da dama, ciki har da shari’a (law), da sauran darussa da ba na fasaha ba.

    Wannan kudiri an gabatar da shi ne kuma ya samu cikakken goyon bayan Sanata Shehu Buba Umar, wanda ya bayyana cewa gyaran zai buɗe sabbin damar karatu da bunƙasa ilimi ga matasa a yankin arewa maso gabas da ma ƙasa baki ɗaya.

    Idan majalisar ta amince da kudirin a karatu na uku, hakan zai ba da damar hukuma ta sauya doka, kuma jami’ar za ta fara karɓar ɗalibai a sababbin fannoni da ba na fasaha kadai ba.

  • Ohanaeze Ta Tsawaita Zanga-Zangar #FreeNnamdiKanuNow Zuwa 25 ga Oktoba, Ta Kaddamar da “Operation Occupy Abuja”

    Kungiyar Ohanaeze Youth Council (OYC), wacce ita ce babbar kungiyar matasan Igbo a fadin duniya, ta sanar da tsawaita zanga-zangar neman a saki Nnamdi Kanu har zuwa ranar Asabar, 25 ga Oktoba, 2025, karkashin taken “Operation Occupy Abuja.”

    Kungiyar ta kuma yi kira ga gwamnati da ta saki duk masu zanga-zangar da aka kama cikin sa’o’i 24, tana gargadi cewa cigaba da tauye ‘yancin jama’a zai iya kara tayar da hankalin al’umma da jefa kasa cikin rashin kwanciyar hankali.

    Ohanaeze ta ce manufar wannan mataki ita ce nuna adawa da tsare Nnamdi Kanu ba tare da hukunci ba, tare da nemi gwamnati ta mutunta doka da hakkin bil’adama.

    Zanga-zangar ta ci gaba da samun karbuwa a sassa daban-daban na kasa, inda kungiyar ta bukaci matasa da su kasance cikin lumana yayin gudanar da tarukan su a Abuja da sauran manyan birane.

  • Kungiyar Concerned Citizens of Bauchi State Ta Mika Ƙorafi Kan Malami a Jami’ar Sa’adu Zungur Saboda Zargin Lalata da Dalibai

    Kungiyar Concerned Citizens of Bauchi State ta aika da wata takardar ƙorafi zuwa ga Shugaban Jami’ar Sa’adu Zungur da ke jihar Bauchi, kan zargin wani malami a Sashen Shari’a (Faculty of Law) na jami’ar, da laifin cin zarafin mata, yin amfani da mukami ba bisa ka’ida ba, da kuma aikata rashin da’a ta fuskar aiki.

    A cikin takardar ƙorafin da ta ke ɗauke da kwanan wata 14 ga Oktoba, 2025, kungiyar ta bayyana cewa ta yanke shawarar sanar da jami’ar ne bisa zargin da ya daɗe ana yi wa malamin na yin lalata da dalibai mata da ke karatu a sashen shari’a na jami’ar.

    Kungiyar ta ce ta ɗauki wannan mataki ne saboda damuwa da kare mutuncin ‘ya’ya mata da dalibai gaba ɗaya, tare da tabbatar da cewa jami’ar ta ci gaba da daidaito da mutunci a idon jama’a.

    A cewar rahoton, akwai hujoji da bayanai na gaskiya da ke nuna cewa malamin yana yin amfani da matsayinsa na malami domin jan hankalin dalibai mata zuwa cikin hulɗar da ta saba doka da ɗabi’a, musamman ta hanyar yaudarar su da alkawarin taimako na ilimi ko damar aiki.

    Kungiyar ta nemi hukumar jami’ar da ta gudanar da bincike mai zurfi domin tabbatar da gaskiyar lamarin, tare da ɗaukar matakin da ya dace idan aka tabbatar da laifin.

    Takardar ƙorafin ta samu sa hannun Shugaban Kungiyar Concerned Citizens of Bauchi State, Comrade A.A. Nuhu, wanda ya bayyana cewa ƙungiyar za ta ci gaba da bibiyar lamarin har sai an tabbatar da adalci ga duk ɓangarorin da abin ya shafa.

  • Mutumin Da Ya Yi Tattaki A Yankin Kudu Ya Samu Kyautar Naira Milyan Goma Daga Gwamna

    Wani mutum dan asalin jihar Ebonyi mazaunin jihar Lagos mai suna Comrade Jeremiah Obaji, wanda ya yi tattaki na tsawon kwanaki 17 daga Ikorodu dake jihar Lagos zuwa garin Abakaliki domin godewa Gwamna Francis Nwifuru kan yadda yayi silar dawowar zaman lafiya a yankin Effium, ya samu kyautar Naira Miliyan Goma daga wajen Gwamnansu na jihar Ebonyi.

    Mutumin dai yayi tafiyar kusan kilomita 600 ne a kafa, a tsawon kwanaki 17 da yayi a hanya sannan kuma ya samu kyakkyawar tarba a wajen jama’ar gari.

    koMutumin Da Ya Yi Tattaki A Yankin Kudu Ya Samu Kyautar Naira Milyan Goma Daga Wajen Gwamnansu

    …ko a cikin masu tattaki a Arewa sun taba samun irin wannan kyautar?

    Dan asalin jihar Ebonyi mazaunin jihar Lagos Comrade Jeremiah Obaji, wanda ya yi tattakin tsawon kwanaki 17 daga Ikorodu dake jihar Lagos zuwa garin Abakaliki domin godewa Gwamna Francis Nwifuru kan yadda ya yi silar dawowar zaman lafiya a yankin Effium, ya samu kyautar naira milyan goma daga wajen Gwamnansu na jihar Ebonyi.

    Mutumin dai ya yi tafiyar kusan kilomita 600 ne a kafa, a tsawon kwanaki 17 da ya yi a hanya. Sannan kuma ya samu kyakkyawar tarba a wajen jama’ar gari.Mutumin Da Ya Yi Tattaki A Yankin Kudu Ya Samu Kyautar Naira Milyan Goma Daga Wajen Gwamnansu

    …ko a cikin masu tattaki a Arewa sun taba samun irin wannan kyautar?

    Dan asalin jihar Ebonyi mazaunin jihar Lagos Comrade Jeremiah Obaji, wanda ya yi tattakin tsawon kwanaki 17 daga Ikorodu dake jihar Lagos zuwa garin Abakaliki domin godewa Gwamna Francis Nwifuru kan yadda ya yi silar dawowar zaman lafiya a yankin Effium, ya samu kyautar naira milyan goma daga wajen Gwamnansu na jihar Ebonyi.

    Koh a cikin masu tattaki a Arewa akwai wanda ya taba samun irin wannan kyautar?

  • HOTUNA: Yadda Al’ummar Musulmi Suka Yi Murnar Samuwar Manzon Allah (SAW) A Kaduna

    Yadda Al’ummar Musulmi Suka Gudanar Da Zagayen Rali Dan Murna Da Samuwar Annabi Muhammad SAW A Cikin Kwaryar Jihar Kaduna.