Blog

  • Dan Majalisa Ya Gina Cibiyar Karatun NOUN a Bauchi

    Hon. Mansur Manu Soro Ya Kafa Cibiyar Karatu ta NOUN a Soro, Jihar Bauchi

    Dan majalisar tarayya mai wakiltar mazabar Darazo–Ganjuwa, Hon. Mansur Manu Soro, ya kaddamar da sabuwar cibiyar karatu ta National Open University of Nigeria (NOUN) a garin Soro, Jihar Bauchi — wani babban ci gaba a fannin ilimi a yankin Bauchi da Arewa maso Gabas baki daya.

    Cibiyar, wacce aka gina a fili mai fadin kusan hektar 10, tana dauke da manyan gine-gine masu inganci da za su iya karbar dalibai fiye da 1,000 a matakin digiri. Hon. Soro ya bayyana cewa wannan cibiyar ita ce irinta ta farko a duk gundumar Sanata ta Bauchi ta Tsakiya (Bauchi Central Senatorial District).

    A wajen kaddamarwar, Hon. Soro ya jaddada cewa yankin Arewa maso Gabas da kuma mazabar Darazo–Ganjuwa na daga cikin wuraren da suka sha fama da wariya da sakaci wajen rabon albarkatun kasa da muhimman ayyukan raya kasa. Ya ce lokaci ya yi da za a mayar da hankali kan ilimi a matsayin hanyar ‘yanci da ci gaba.

    Bude cibiyar NOUN a Soro, wacce ita ce ta farko a dukan Bauchi Central Senatorial District, na daga cikin muhimman ayyukan tarihi da muka gabatar a fannin ilimi.

    Mun fara irin wannan aiki a shekarar 2021 a matakin firamare da sakandare, inda muka kafa makarantu hudu (4) na Gifted Senior Secondary Schools da kuma makarantar firamare ta musamman guda (1) a Sade, Soro, Kafin Madaki, Darazo da Lanzai.”

    Hon. Soro ya kara da cewa yana da niyyar ci gaba da inganta fannin ilimi musamman a kauyuka da ke da karancin damarmaki, domin tabbatar da cewa kowanne yaro yana da damar samun ilimi mai inganci.

    Ana sa ran cibiyar NOUN da ke Soro za ta fara karbar dalibai nan gaba kadan, tare da samar da damar karatu ga wadanda ba su da ikon zuwa jami.

  • Shekaru Biyu Na Cigaba a Bangaren Albarkatun Kasa a Jihar Bauchi

    Jihar Bauchi ta cika shekaru biyu da aiwatar da gagarumin sauyi a bangaren harkokin albarkatun kasa, inda aka samu labarin sabuwar tafiya mai cike da hangen nesa, sauye-sauyen manufofi da kuma jarin da bai taba kasancewa ba a baya. A tsakiya na wannan tafiya akwai Gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Abdulkadir Mohammed (Kauran Daular Usmaniyya), tare da wakilinsa a bangaren, Kwamishinan Habbankunan Halittu, Hon. Muhammad Maiwada Bello.

    Tun daga nada shi a watan Agusta 2023, Hon. Maiwada Bello ya kawo sabon salo a tsarin kula da albarkatun kasa a matakin jiha, inda aka farfado da bangaren da aka taba dauka marar amfani, zuwa daya daga cikin ginshikan bunkasar tattalin arzikin jihar, janyo jarin waje da kuma ci gaban mutane.

    A watan Afrilu 2025, Ma’aikatar ta shirya taron horas da ma’aikata na tsawon mako biyu a Hotel Zaranda, inda aka koyar da sabbin dabarun hakar ma’adinai. Haka kuma gwamnati ta sayi kayan aiki na zamani da motoci guda hudu domin bunkasa ayyukan BOGAA da BAMSEL.

    Har ila yau, an dauki sabbin ma’aikata 19 a BAMSEL/ma’aikatar da kuma 43 a Bauchi Oil & Gas Academy (BOGAA), tare da aiwatar da tsari na tabbatar da gaskiya a biyan albashi.

    Wani babban nasara kuma shi ne kafa BOGAA a Alkaleri, cibiyar da ta samu sahalewar NBTE tare da hadin gwiwa da kamfanoni irin su Petro-Edu. Har yanzu, sama da dalibai 530 ne suka kammala karatu, yayin da gwamnatin jihar ta ware fiye da ₦6 biliyan domin gina sabon babban harabar makarantar.

    Baya ga haka, a watan Disamba 2023, aka kafa dokar Mining Consent Letter Policy, inda aka dakatar da sarakunan gargajiya daga bayar da izinin hakar ma’adinai ba tare da kulawar gwamnati ba. Wannan ya taimaka wajen dakile barna, hana ayyukan ba bisa ka’ida ba da kuma karuwar kudaden shiga.

    Ma’aikatar ta kuma fara tattara bayanan duk masu hakar ma’adinai na gargajiya tare da basu damar shiga tsarin gwamnati. Wannan ya taimaka wajen samar da ayyukan yi, karuwar kudaden shiga da kuma rage matsalolin tsaro.

    Daga shekarar 2023 zuwa yanzu, sama da kamfanoni 100 aka yi musu rijista da ma’aikatar, yayin da kudaden shiga suka tashi daga sifili zuwa miliyoyin naira a kowane wata.

    A gefe guda kuma, an kafa hadin gwiwa tsakanin BAMSEL da kamfanin Indiya Prompt Workman Ltd, da darajar sama da dala miliyan 5, domin bude cibiyar kasuwancin ma’adinai ta kasa da kasa a Bauchi.

    Babban abin da aka fi yaba shi ne jarin sama da dala biliyan 2 da aka samu a bangaren hakar ma’adinai da masana’antu. A Toro LGA, aikin $50m Rare Earth Elements Factory ya kusa kammaluwa, yayin da a Gwana, Alkaleri LGA, ake aikin gina cibiyar siminti mai darajar $1.5bn wacce za ta samar da wutar lantarki 150 MW da dubban ayyukan yi.

     A watan Mayu 2025, Hon. Bello ya jagoranci tawagar jihar zuwa babban taron hakar ma’adinai na CIM CONNECT a Montreal, Kanada, tare da wasu kasashe kamar China da Afirka ta Kudu, inda aka kara fito da Bauchi a matsayin daya daga cikin wuraren da ake sa ran samun manyan jarin kasa da kasa.

    Da yake magana, Hon. Bello ya ce:

    “Wadannan ayyuka ba wai kawai ayyukan yau da kullum ba ne, su ne ginshikan gado da za su tabbatar da makomar Bauchi a doron cigaba, dorewa da kirkire-kirkire.”

    A halin yanzu, masana harkokin ma’adinai na ganin Bauchi a matsayin jagora a fagen hakar ma’adinai a Najeriya, abin da suka danganta da hangen nesa da jagorancin Gwamna Bala Mohammed da kuma kwazon Kwamishina Maiwada Bello.
    (more…)

  • Rundunar ’Yan Sanda ta Kaduna Ta Ce Tsohon Gwamna El-Rufai Ya Shigo Da ’Yan Daba Da Suka Tarwatsa Taron Siyasa

    Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Kaduna ta bayyana cewa ta kaddamar da bincike kan wani taron siyasa da tsohon gwamnan jihar, Malam Nasir El-Rufai ya shirya, wanda ya rikide zuwa tashin hankali da harbe-harbe.

    SaharaReporters ta ruwaito cewa wasu ’yan daba da ake zargin gwamnatin jihar ta dauko su sun kai farmaki a wurin taron hada kan jam’iyyar Social Democratic Party (SDP) da African Democratic Congress (ADC) a cikin garin Kaduna, inda suka jikkata mutane da dama.

    Rahotanni sun nuna cewa taron hadin gwiwar jam’iyyun SDP da ADC karkashin jagorancin Malam Nasir El-Rufai, tsohon gwamnan jihar, shi ne ya rikide zuwa tashin hankali har ya haifar da tarzoma da harbe-harben bindiga.

  • Zamani TV ta ƙaddamar da Sabon Shafin Labarai a Yanar Gizo

    Kamfanin yada labarai na Zamani TV ya ƙaddamar da sabon shafin yanar gizo na musamman domin kawo wa al’umma sahihan labarai cikin sauƙi da sauri. Wannan mataki wani ɓangare ne na ci gaba da inganta hanyoyin sadarwa da yada bayanai na zamani ga masu sauraro da masu kallo a sassa daban-daban na ƙasa da ƙetare.

    Shafin yanar gizon zai riƙa bayar da labarai kan fannoni daban-daban kamar su siyasa, tattalin arziƙi, al’adu, kiwon lafiya, wasanni, da kuma rahotanni na musamman da suka shafi rayuwar yau da kullum.

    Shugabannin kamfanin sun bayyana cewa ƙaddamar da shafin labaran ya nuna jajircewar Zamani TV wajen amfani da fasahar zamani don isar da sahihan bayanai cikin gaggawa, tare da ƙarfafa yadda matasa da sauran al’umma za su iya samun damar labarai kai tsaye ba tare da wahala ba.

  • Bala Wunti Ya Karyata Maganar Tsayawa Takarar Gwamna a Bauchi, Yace Yana Cigaba da Tuntuba

    Dr. Bala Wunti ya bayyana cewa bai taba ayyana tsayawa takarar Gwamnan Bauchi ba, sabanin jita-jitar da ake yadawa a kafafen sada zumunta cewa ya amince zai tsaya takara a 2027.

     

    A cikin wata sanarwa da ya fitar, Dr. Wunti ya ce: “Ina matuƙar godiya ga kiraye-kiraye da dama da al’umma ke yi na shiga siyasa, amma a halin yanzu ina ci gaba da tuntuba da muhimman shugabanni. A lokacin da ya dace zan bayyana matsayina na a hukumance.

     

    Ya kara da cewa duk wata sanarwa daga gare shi za a fitar ta ne ta hanyar shafukan sada zumunta na hukuma da aka tabbatar da sahihancinsu, tare da jan hankalin jama’a cewa babu wanda ya samu izinin yin magana a madadinsa.

     

    Dr. Bala Wunti ya gode wa duk masu kawo wannan batu a gareshi tare da yi wa jihar Bauchi da al’ummarta fatan alkhairi.

  • DA DUMI-DIMI: Kotun Bauchi Ta Baiwa EFCC Damar Ci Gaba da Binciken Hamza Koshe da Kamfaninsa

    Alkalin Babbar Kotun Jiha dake Bauchi, Mai Shari’a Aliyu Baba Usman, ya baiwa Hukumar (EFCC) damar ci gaba da bincike a kan Alhaji Hamza Koshe da kamfaninsa mai suna Pentech Engineering Nig. Ltd.

     

    Rahotanni sun bayyana cewa a ranar 23 ga Satumba, 2024, Koshe ya shigar da kara a kotu yana neman a hana EFCC ta ci gaba da bincike da gurfanar da shi tare da kamfaninsa.

     

    Yayin yanke hukunci a ranar 30 ga Yuli, 2025, Mai Shari’a Usman ya bayyana cewa: “Wannan kotu da sauran kotunan shari’a ba su da hurumin hana hukumomin tsaro da doka gudanar da ayyukansu na bincike da gurfanarwa, musamman a kan laifukan rashawa, almundahana, halatta, da sauran manyan laifukan tattalin arziki.”

     

    Saboda haka, kotu ta baiwa EFCC damar ci gaba da bincike a kan Koshe.

     

    Tun da farko EFCC ta gayyaci Koshe domin amsa tambayoyi, amma maimakon ya amsa, sai ya garzaya kotu ya shigar da kara.

     

    Zamani TV