Zamani TV ta ƙaddamar da Sabon Shafin Labarai a Yanar Gizo

Kamfanin yada labarai na Zamani TV ya ƙaddamar da sabon shafin yanar gizo na musamman domin kawo wa al’umma sahihan labarai cikin sauƙi da sauri. Wannan mataki wani ɓangare ne na ci gaba da inganta hanyoyin sadarwa da yada bayanai na zamani ga masu sauraro da masu kallo a sassa daban-daban na ƙasa da ƙetare.

Shafin yanar gizon zai riƙa bayar da labarai kan fannoni daban-daban kamar su siyasa, tattalin arziƙi, al’adu, kiwon lafiya, wasanni, da kuma rahotanni na musamman da suka shafi rayuwar yau da kullum.

Shugabannin kamfanin sun bayyana cewa ƙaddamar da shafin labaran ya nuna jajircewar Zamani TV wajen amfani da fasahar zamani don isar da sahihan bayanai cikin gaggawa, tare da ƙarfafa yadda matasa da sauran al’umma za su iya samun damar labarai kai tsaye ba tare da wahala ba.

Comments

7 responses to “Zamani TV ta ƙaddamar da Sabon Shafin Labarai a Yanar Gizo”

Leave a Reply