Category: Siyasa

  • Elder Karofi ya caccaki Sanata Shehu Buba kan kama matasa

    Wani jigo a cikin matasan jihar Bauchi, Elder Karofi, ya yi kakkausar suka ga Sanata Shehu Buba bisa zargin yin amfani da mukaminsa wajen kama matasa a fadin jihar.

    A cikin wani faifan bidiyo da ya wallafa a safiyar yau, Elder Karofi ya zargi sanatan da amfani da karfin iko wajen tsoratar da matasa maimakon yin aiki tare da su don ci gaban siyasa da dimokuraɗiyya.

    Ya ce siyasa rigar ’yanci ce wacce ta baiwa kowa damar bayyana ra’ayinsa, ba doka ta kama ko tsoratar da mutane ba.

    “Shehu Buba, me kake nema da matasan Bauchi? Kullum sai ka kama wannan ko wancan – wannan abin naka ya yi yawa. Kai ba kai kaɗai ba ne, siyasa ba mallakar mutum ɗaya ba ce. Idan bada ka iya jure adawa ba, ka hakura da siyasa gaba ɗaya,” in ji Elder Karofi a cikin bidiyon.

    Elder Karofi ya kara da cewa matasan Bauchi ba sa tsoron kowa, kuma za su ci gaba da fadin ra’ayinsu da kalubalantar duk wani dan siyasa da ke kokarin tauye hakkokinsu, har ma da Sanata Shehu Buba.

    Ya kuma yi gargadi ga sanatan da ya daina tsoratar da matasa, yana mai cewa:

    “Muna maka gargadi, ka daina tsoratar da matasan Bauchi. Ka bar su su taka rawarsu cikin ’yanci da dimokuraɗiyya.”

  • Bala Wunti Ya Karyata Maganar Tsayawa Takarar Gwamna a Bauchi, Yace Yana Cigaba da Tuntuba

    Dr. Bala Wunti ya bayyana cewa bai taba ayyana tsayawa takarar Gwamnan Bauchi ba, sabanin jita-jitar da ake yadawa a kafafen sada zumunta cewa ya amince zai tsaya takara a 2027.

     

    A cikin wata sanarwa da ya fitar, Dr. Wunti ya ce: “Ina matuƙar godiya ga kiraye-kiraye da dama da al’umma ke yi na shiga siyasa, amma a halin yanzu ina ci gaba da tuntuba da muhimman shugabanni. A lokacin da ya dace zan bayyana matsayina na a hukumance.

     

    Ya kara da cewa duk wata sanarwa daga gare shi za a fitar ta ne ta hanyar shafukan sada zumunta na hukuma da aka tabbatar da sahihancinsu, tare da jan hankalin jama’a cewa babu wanda ya samu izinin yin magana a madadinsa.

     

    Dr. Bala Wunti ya gode wa duk masu kawo wannan batu a gareshi tare da yi wa jihar Bauchi da al’ummarta fatan alkhairi.