Kamfanin Zamani TV zai gudanar da wani babban taron godiya da karramawa ga abokan cinikayyarsa, mabiyanta, abokan hulɗa da masu goyon bayanta, domin nuna godiya bisa irin gudummawar da suke bayarwa wajen ci gaba da bunƙasa kafar watsa labaran.
An shirya taron ne domin bikin Ranar Abokan Cinikayya ta Duniya (International Customer Service Day), tare da nuna godiya ga waɗanda suka kasance cikin tafiyar Zamani TV tun daga kafuwarta.
Taron zai gudana ne a Laraba, 7 ga Oktoba, 2026, da ƙarfe 10:00 na safe, a International Conference Center ICC Bauchi
Taron wata dama ce ta musamman ta yaba wa abokan ciniki da masu goyon bayan kafar bisa amincewa da suke yi da ita da kuma irin gudummawar da suke bayarwa wajen ci gabanta.
